ZUCIYA TAGAJI DA JIRA 5
📖 Sashe na 5: Gari Ya Farka da Wani Labari Gari na kwana ya tashi da sabon jita-jita: > “An ce Hauwa tana da ciki!” “Wai ba Muhammad ne ya yi ba, wani soja ne daga Kaduna!” “Lallai ‘yar liman ta lalace.” Kowanne bako yana da labarinsa. Amma babu wanda ya tambaye Hauwa kanta. Muhammad ya ji labarin a kasuwa. Jikinsa ya yi sanyi. Ya hau mashin ya nufi gidan liman. Sai dai kafin ya karasa, ya ci karo da Hauwa a bakin hanya — tana d’auke da jakar kaya da jariri a hannunta. Jariri? A'a — kayan da za ta kai asibiti. Suka hada ido. Ta ce masa cikin sanyi: > “Zuciyata ta gaji da jira, Muhammad. Kuma lokacin jira ya kare.” Ta wuce, ta bar shi tsaye, kamar gunki, babu motsi.