ZUCIYA TAGAJI DA JIRA 2
---
📖 Zuciyata Ta Gaji Da Jira
Sashe na 2: Duhu Bayan Shiru
Kwana uku suka wuce. Muhammad bai dawo ba. Hauwa na nan a karkashin baobab — tana jira, tana fata. Amma babu motsin takalmi. Babu shi.
A cikin gari, shirin bikin Muhammad da Amina ya kankama. Ana ganguna, ana dinki, ana shela.
> “Yanzu dan Alhaji Garba zai auri diya mai iko,” mutane ke cewa.
Amma babu wanda ya tambayi abin da Muhammad yake so.
Da yamma, Hauwa na zaune a bakin rafi, Muhammad ya iso.
> “Me ya sa ba ka tsaya ka fadi gaskiya ba?” ta tambaya cikin sanyin murya.
> “Hauwa… na so... amma mahaifina—”
> “Kada ka yi karyar ‘bani da zabin da ya fi wannan’,” ta katse shi. “Ka zabi suna fiye da soyayya.”
Kalaman ta sun sare shi.
---
Washegari da safe, Hauwa ta je asibiti — ita kadai.
Ta mika wata takarda ga nas da cewa:
> “Don Allah, ina bukatar sanin gaskiya... Ina dauke da ciki ne ko kuwa a'a?”
To be continue....
Comments
Post a Comment