ZUCIYATA TA GAJI DA JIRA 1
“Zuciyata Ta Gaji Da Jira"
📖 Zuciyata Ta Gaji Da Jira
Sashe na 1: Sirrin da Wata ta Ganewa
Baobab — itacen tarihi a tsakiyar kauyen Gargwarje — ya sha ganewa soyayya da kukan zuciya. Amma babu kamar na Hauwa da Muhammad.
Hauwa, ‘yar limamin kauyen, budurwa ce mai kunya da mutunci. Kowane safiya tana tafiya da roba a hannunta, fuskarta cike da nutsuwa. Mafi yawan samari sun ce: “Wannan ita ce matar aure, ba budurwa ba.”
Muhammad, dan Alhaji Garba, ya dawo daga jami’ar Ahmadu Bello (ABU). Kyakkyawan saurayi, mai natsuwa da ilimi. Amma duk lokacin da ya ganta a bakin rafi, zuciyarsa na karaya.
Ranar wata ya cika, suka hadu a karkashin itacen baobab.
> “Hauwa,” inji Muhammad, “na zo ne in fada miki gaskiya. Ina sonki. Ina son na aure ki.”
Hauwa ta sunkuyar da kai, zuciyarta na bugawa da karfi.
> “Amma mahaifinka… bazai amince da ni ba.”
> “Zan aure ki ko da ya ki,” Muhammad ya fada da tabbaci. “Ke nake so.”
To be continue...
Amma soyayya ba ta da sauki. Washegari gari ya dauka da labari:
Muhammad zai auri Amina, ‘yar sanata daga Kaduna.
Hauwa ta ji labari daga yaron makotansu. Ba ta yi kuka ba. Ba tukuna.
Sai ta koma karkashin baobab, ta zauna cikin shiru. Sai kawai ta ce:
> “Ashe haka soyayya take? Alkawari da dare, cin amana da safe…”
Comments
Post a Comment